19 Satumba 2026 - 21:00
Source: ABNA24
Saudiyya: Gobarar Tankin Mai Na Aramco Ta Katse Zirga-Zirgar Jiragen Filin Jirgin Sama Riyadh

Gobarar da ta tashi a wani tankin mai na Aramco kusa da filin jirgin sama na Riyadh tare da bayar da gargaɗin sama da kuma jin ƙarar fashewa ya haifar da jinkiri da soke tashi da saukar wasu jirage na cikin gida da na ƙasa da ƙasa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na "King Khalid" a Riyadh a yau Asabar ya fuskanci Babbar togaciya a tafiyar jirage. Matsalar da ta haifar da dogon jinkiri da soke wasu jirage. An wallafa waɗannan bayanai ne bisa ga bayanan shafin yanar gizo na "Flightradar24" ƙwararre kan lura da zirga-zirgar jiragen sama.

Dangane da rahoton jaridar "Al-Arabi Al-Jadeed", wannan shafin ya sanya filin jirgin sama na Riyadh a matakai mafi girma na rikici. A lokaci guda, kamfanin dillancin labarai na Faransa bisa ga rahoton da mazauna suka bayar ya ba da labarin ganin hayaki kusa da filin jirgin sama na Riyadh kuma ya bayyana cewa wakilin wannan kamfanin ya ga harshen wuta a cikin wani tankin mai na kamfanin Aramco kusa da filin jirgin sama na Riyadh yayin da jami’an kashe gobara ke ƙoƙarin shawo kan gobarar.

Waɗannan damuwa sun shafi jirage na cikin gida da na ƙasa da ƙasa kuma sun haifar da jinkiri na sa'o'i da canza hanyar wasu jirage masu shigowa. Har ila yau, dakunan filin jirgin sama na Riyadh cike suke da fasinjoji da ke jira a tantance sabon lokacin jirage ko samun bayani daga kamfanonin jiragen sama.

Kamfanonin jiragen sama sun roƙi fasinjoji da kafin tafiya zuwa filin jirgin sama na Riyadh, su duba yanayin jirginsu ta hanyar manhajoji da shafukan yanar gizo na hukuma kuma su tuntuɓi cibiyoyin sabis na abokan ciniki don hana cunkoso da ya samo asali daga jinkiri da soke jirage.

Gargaɗin Sama Kafin Fashewa A Riyadh

tabarbarewar tafiyar jirage ta faru ne sa'o'i kaɗan bayan da hukumomin Saudi Arabiya a babban birnin suka bayar da gargaɗin ta sama.

Mazauna yankuna da dama na Riyadh yan dakiku kaɗan kafin ƙarfe uku na safe a lokacin gida sun sami saƙo wanda a cikinsa aka yi gargaɗi game da kasancewar barazanar harin sama na ƙiyayya kuma an roƙe su da su kasance a cikin gidajensu.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa ya ba da rahoton cewa wakilan wannan kamfanin bayan bayar da gargaɗin, sun ji ƙarar fashewa biyu kuma kusan rabin sa'a bayan haka, hukumar kare fararen hula ta Saudiyya ta bayyana ƙarshen gargaɗin. Mazauna arewa da tsakiyar Riyadh ma sun ba da labarin jin gargaɗin da girgizar tagogi kuma sun kwatanta yanayin a matsayin mai ban tsoro da firgici.

Ɗaya daga cikin mazauna mai shekaru 27 na arewacin Riyadh ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Faransa: Na ji gargaɗin sannan tagogina sun girgiza. Tabbas abin ban tsoro ne. Ban yi tsammanin irin wannan ba. Wani kuma ya kwatanta abin da ya faru a matsayin mai ban tsoro.

Wata mata mazauniyar babban birnin Saudiyya da mijinta ma sun gaya wa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa sa'o'i kaɗan bayan jin ƙarar fashewar a Riyadh, sun ga hayaki yana tashi kusa da filin jirgin sama.

Wani mazaunin tsakiyar Riyadh ya bayyana: Na damu sosai, musamman da yake sabanin lokutan da suka gabata, ba a bayar da alamar ƙarshen haɗari nan take ba.

Raguwar Fitar Mai Da Kayayyaki Ta Hanyar Babal-Mandab

Tsanantar tashin hankali a Tekun Maliya da mashigar Babal-Mandab ya haifar da raguwar zirga-zirgar fitarwar kayyaki da mai daga Saudiyya. Kamfanin "Kpler" da ke aiki a fannin lura da jigilar ruwa, ya bayyana cewa jiragen ruwa biyar kawai da ke ɗauke da kayayyakin Saudiyya cikin kwanaki bakwai da suka gabata ne suka fita daga Tekun Maliya ta mashigar Babal-Mandab. Adadin da bai kai kashi ɗaya cikin uku na matsakaicin mako-mako da aka rubuta tun watan Janairu da ya gabata ba.

Mashigar Babal-Mandab wata mashiga ce mai mahimmanci wadda ke haɗa Tekun Maliya da Tekun Indiya kuma tana ba da damar jigilar kaya tun daga makamashi da sauran kayyakin masrufi tsakanin Asiya da Turai ta tashar Suez.

Muhimmancin wannan mashigar ga Saudiyya ya ƙaru ne a yanayin da tun farkon yaƙin Amurka kan Iran, aka sanya ƙuntatawa kan tafiyar jiragen ruwa daga mashigar Hormuz.

..............................

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha